Jami’ai a Bangaladesh sun ce wata gobara ta yi sanadiyar mutuwar 78  a gundumar Birnin Dhaka mai tsohon tarihi a kasar.

Gobarar dai ta tashi ne cikin dare a wani gida da aka jibge wasu kayayyaki, wadanda yawanci makamashin wuta ne.

Ana tsammanin wasu mutane da suka halarci wata liyafar aure na daga cikin wadanda suka mutu, sannan kawo yanzu ba asan abun da ya jawo tashin gobarar ba.

Ana yawan samun tashin gobara a manyan gine-gine da ke yankunan da jama’a ke da yawa a Bangladesh, inda ake ganin rashin kula da bin tsarin dokoki ke janyo tashin gobarar.

A ranar Lahadin da ta gabata, wata gobara ma ta tashi a wata unguwar marasa galihu da ke birnin Chittagong da ke gabar teku,wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9.

‘Yan kwana-kwana sun yi ta aiki fiye da sa’’o’i biyar domin kashe gobarar, lamarin da ya gamu da cikas sakamakon cinkoson gidajen da kuma rashin isasshen ruwan kashe gobarar.