Kwamandan hukumar kwastom na shiyyar Apapa da ke jihar Legas Bashir Abubakar, ya ce yankin da ya ke jagoranta ya tara kudaden shiga da suka kai Naira biliyan 61 a cikin watanni biyu da suka gabata.

Bashir Abubakar ya bayyana haka a Legas ranar Litinin din da ta gabata inda ya kara da cewa, sun samu damar tara harajin ne sakamakon yadda ake bin diddikin aikin kamar yadda doka ta tanada.

Hukumar ta kara da cewa, a tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, ta kwace wasu sundukai 24 makare da Tumatari da kuma man girki, wanda aka biya kudaden shiga har fiye da Naira miliyan 200.

A karshe hukumar ta yi kira ga jami’an ta su hada kai domin samun nasara a koda yaushe.