Wani dan majalisar dokokin kasar Iraki Muhammad Al-Baldawi ya gargadi Amurka a kan yunkurin ta na sakin fursunonin ‘yan ta’adda a cikin kasar domin sa ke ba su damar farfadowa.

Muhammad Al-Baldawi ya nuna dawumar sa a kan yadda Amurkan ta ke son maimaita abun da ya faru a gidajen kurkukun Abu Guraib al-Tasfirat, da Takrit.

Dan majalisar ya yi nuni da yadda Amurka ta fusata, sakamakon yadda Irakawa sun ki yarda su ba ta damar kafa sansanin soja a kasar, sannan ya kara da cewa, da akwai ‘yan ta’adda masu yawa a cikin gidajen kurkukun Iraki wadanda aka fitar da su domin samar da gibin tsaro a kasar.

A bangare guda kuwa, wani kwamandar rundunar sa kai ta Hashdus-Sha’abi Qasim Muslih, ya ce Amurkan ta yi wa ‘yan ta’adda nuni akan su sake farfado da ayyukan su na ta’addanci a kasar.