Shugaba Muhammadu Buhari ya ba Turkiya tabbacin cewa, Najeriya za ta ci gaba da taimaka ma ta a yakin da take yi da ayyukan ta’addanci, yayin da ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai birnin Santanbul a Lahadin nan.

Shugaba Buhari ya yi tir da harin wanda ya lakume rayukan mutane 6 tare da jikkata wasu da dama a kan titin Istiklal mai cike da zirga-zirgar jama’a a tsakiyar birnin Santanbul.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana harin a matsayin abin kyama da kuma rashin jarumta.

Najeriya dai na cikin jerin kasashen Afrika da ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren Boko Haram da kuma ‘yan bindigar da ke satar mutane suna karbar kudin fansa.