An yaba wa ma’aikatan hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga manyan makarantu da ke Kaduna wato JAMB a kan yadda su ke gudanar da aikin su.

Wani dan jarida da ya ziyarci ofishin hukumar ya bayyana haka,  inda ya ce  lokacin da ya ziyarci ofishin hukumar, ma’aikatan ta sun tarbe shi hannu biyu ba tare da nuna masa bambancin kabila ko addini ba.

Ya ce ma’aikatan hukumar,  a kowane lokaci su na cikin aiki tare da karbar dalibai domin magance wata matsala da su ke fuskanta.

Dan jaridar da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya bukaci sauran hukumomin ilimi su yi koyi da ma’aikatan hukumar JAMB, domin samun ci-gaba mai dorewa.

A karshe ya ce haka ake bukatar ma’aikata a kowane lokaci su kasance cikin aiki da nuna kwarewa,  ba tare da nuna wariya ga sauran abokan aikin su ba.