Kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke Abuja, ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Haka kuma, kotun ta yanke hukuncin cewa ba jam’iyyar APC da dan takarar ta Gboyega Oyetola ne su ka lashe zaben ba, don haka ta kwace nasarar da aka ba jam’iyyar bayan zaben jihar zagaye na biyu.
Dan takarar jamiyar APC Gboyega Oyetola dai, ya doke abokin takarar sa na jamiyar PDP Ademola Adeleke a zaben da aka sake gudanarwa zagaye na biyu da tazarar kuri’u 483.
Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta sanar da sakamakon zaben bayan karashen zaben da aka gudanar a wasu mazabu da aka dakatar da zaben su.
Sai dai bayan sanar da sakamakon zaben, Sanata Adeleke da jam’iyyar PDP sun garzaya kotun saurarrn korafe-korafen zaben gwamnan, inda su ka ce ba su amince da sakamakon zaben ba.