Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta dakatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP bisa hujjar rashin gudanar da zaben fidda gwani.

A Zaman sauraren shari’ar, Alkali Ambrose Lewis, ya ce Jam’iyyar PDP ba ta fitar da Abba Kabir Yusuf a tsarin da ya dace wajen fitar da dan takara ba.

Lauyan masu shigar da kara Kabiru Usman, ya ce dole ne Jam’iyyar PDP ta sake tsaida dan takara na daban gabanin zaben gwamnoni a ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai lauyan PDP Bashir Yusuf, ya ce hukuncin kai tsaye bai shafi Abba Kabir Yusuf ba illa jam’iyyar PDP, wadda ke da zabin sake gudanar da zaben fidda gwani. Hukuncin Kotun dai ya na da nasaba da karar da Al-Amin Little ya shigar, ya na kalubalantar matakin da Jam’iyyar ta bi wajen fitar da dan takarar gwamna a jihar Kano.