Alamu na nuna cewa, wasu kwamishinonin zabe na jiha da na kasa za su yi murabus daga matsayin su, biyo bayan zargin barazana da tozarci da kuma barazanar da rayuwar su ta fuskanta daga hukumomin tsaro a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisun tarayya.
Kwamishinonin dai sun yi zargin cewa, sun kasance masu duba ga Shugaban hukumar a kan tarin hadurran da rayuwar su ke ciki, sai dai shi kan sa ya na fuskantar matsi da yawan hare-hare daga manyan mutane.
Wasu jami’an zabe na jiha da na kasa sun kasance a cikin tsoron cewa, ana iya kai masu mumunan hari a ranar 9 ga watan Maris, yayin da za a gudanar da zaben gwamna da na majalisar jiha.
Wasu majiyoyi sun ce an yi garkuwa da wasu jami’an zabe a lokacin zaben, yayin da jami’an tsaron da za su ba su kariya su ka yi batan-dabo a lokacin da su ke tsananin bukatar su.
Majiyoyin sun kuma zargi hukumomin tsaro, ciki har da rundunar soji da sauran hukumomi da jan hankalin jami’an zabe, yayin da su ke ikirarin ba su kariya, a lokaci guda kuma su ka rika rarraba kayayyakin zabe ga ‘yan siyasa ba bisa ka’ida ba.